Kotu ta ci tarar Trump sama da dala miliyan 350 saboda zamba
An ci tarar tsohon Shugaban Amurka Donald Trump kusan dala miliyan 355 a birnin New York a jiya Juma’a bayan gano cewa ya na da hannu a batutuwa da suka jibanci zamba a masana’antarsa mai suna Trump Organisation,hukuncin na kuma tabbatar da dakatar da tsohon shugaban Amurka na tsawon shekaru uku daga duk wani harkokin kasuwanci a jihar New York.
Wallafawa ranar:
Wannan matakin da ba a taba ganin irinsa ba, wani rauni ne ga tsohon shugaban Amurka, wanda ke da burin sake tsayawa takarar zaben Shugabancin kasar na watan Nuwamba r 2024.
A cikin wata takarda mai shafuka 92 daga kotu, Alkalin kotun kolin Jihar New York, Arthur Engoron, ya sanar da sauke tsohon Shugaban kasar Donald Trump daga “duk wani shugabanci na kamfani ko wata hukuma a New York na tsawon shekaru uku” tare da ba da umarnin biyan dala miliyan 354.86.
Babbar Lauyan jihar Letia James ta shigar da kara a kansa a watan Oktoba 2022 a kan tsohon shugaban kasar tare da ’ya’yansa manya guda biyu Donald Jr da Eric Trump da kuma danginsu.
A wani martani na farko, Donald Trump ya yi tir da hukuncin ga baki daya, da kuma bayyana cewa ana kokarin shafa massa kashin kaji da kuma hana shi tsayawa takara a zaben kasar a jam'iyyar Republican.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu