Isa ga babban shafi

Donald Trump ya lashe zaben fidda gwanin jihar Iowa

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya lashe zaben fidda gwanin jihar Iowa, nasarar da ta tabbatar da matsayinsa na dan takarar da ke kan gaba wajen neman tikitin jam'iyyar Republican don sake tsaya mata takara a zaben shugabancin kasar da za a yi a cikin wannan shekara .

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump. AP - Charlie Neibergall
Talla

Yayin zaben fidda gwanin na Iowa a ranar Litinin, Trump ya samu nasarar kayar da tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley da gwamnan jihar Florida Ron DeSantis.

Trump ya lashe kashi 51 na yawan kuri'un da aka kada, yayin da DeSantis ya samu kashi 21, Haley kuma ta samu kashi 19, lamarin da ya bai wa tsohon shugaban damar kusantar samun tikitin takarar neman jagorancin Amurka a karo na uku a jere.

Trump na ci gaba da samun karbuwa a jam'iyyarsa ta Repulican duk da cewa yana fuskantar shari'a kan tuhume-tuhumen aikata ba dai dai ba, ciki kuwa har da zarginsa da yin karya wajen kara yawan dukiyar da ya mallaka don kara darajar kasuwancinsa .

A wannan Talata ake sa ran tsohon shugaban Amurkan zai sake bayyana gaban kotu a birnin New York, yayin da alkalai za su tantance ko zai biyya diyyar dala miliyan 5, bisa laifin cin zarafi da bata masa suna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.