Isa ga babban shafi

Miyagun duniya sun samu ribar dala biliyan 236 daga bautar da mata

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, miyagu a sassan duniya sun samu ribar kudin da ta kai dala biliyan 236 bayan sun tilasta wa 'yan mata shiga aikin karuwanci kamar yadda wani rahoton Majalisar ya nuna a wannan Talatar.

Wasu 'yan mata da ake wayar musu da kai don hana su shiga aikin bauta da karuwanci.
Wasu 'yan mata da ake wayar musu da kai don hana su shiga aikin bauta da karuwanci. Reuters/Katy Migiro
Talla

Miyagun na cin zarafin 'yan ci-rani da suke kwace musu 'yan kudadensu na albashi da suka tara domin tura wa iyalansu, yayin da suke raba su da halastattun ayyukansu na kwadago suna bautar da su, lamarin da ke bai wa miyagun damar kauce wa biyan haraji.

Hukumar Kula da Kwadago ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu karuwar haramtattun kudaden da wadannan miyagun ke samu da kashi 37% ko kuma dala biliyan 64, idan aka kwatanta da alkaluman da aka tattara a shekarun baya. Alkaluman sun kuma nuna cewa, adadin mutanen da ake cin zarafinsu ta wannan hanyar sun karu.

Hukumar ta ILO ta ce, irin wannan aikin bautar na samar wa cin hanci da rashawa gindin-zama da kuma karfafa gungun miyagun da ke cin gajiyar haramtaccen kudin da suke samu.

Darekta Janar ha hukumar ILO, Gilbert Houngbo ya bukaci kasashen duniya da su bada goyon baya domin yakar wannan muguwar  dabi'ar.

Mutanen da ake bautar da su, na fuskantar barazana kala-kala da suka hada da kwace musu albashinsu da gayya. Aikin bauta na dawwamar da da'irar talauci da cin zarafi da kuma haifar da miki a zukatan bil'adama. Inji Houngbo

A cikin shekarar 2021, an kiyasta cewa, mutane miliyan 27.6 na gudanar da aikin bauta, alkaluman da ke nuna cewa, an samu karuwar kashi 10% cikin 100% na wannan adadin cikin shekaru biyar na baya.

Hukumar ILO ta ce, yankin Asia da Pacific na da sama da rabin alkaluman da aka ambata, yayin da nahiyar Afrika da yankin Amurka da Tsakiyar Turai kowacce daga cikinsu ke da kimanin kashi 13% zuwa kashi 14%.

Kashi uku cikin hudu na wadannan mutanen, an tilasta musu shiga karuwanci kuma akasarinsu 'yan mata ne da  kananan yara mata a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.