A ranar 16 ga Watan Afrilu ne ake nada sabon shugaban bankin Duniya, daya daga cikin manyan hukumomin kudade na duniya. Kuma Jim Yong Kim ne ya lashe zaben bayan fafatawa da Ngozi Ikonjo Iweala ta Najeriya.
Kasar Amurka tafi kowacce kasa jari a Bankin, kuma an kwashe shekaru 40 Amurka na Jagorancin Bankin.
A bana an samu kasashen da ke nuna mata yatsa a ido, domin kasashe masu tasowa suna ganin lokaci ya yi da ya kamata a samu sauyi, abinda ya sa aka samu Yan takara biyu da ke kalubalantar wanda Amurka ta tsayar.
A cikin wannan shirin, Bashir Ibrahim Idris tare da bakin sa sun duba wannan fafutuka da kuma tasirin na Bankin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu