Isa ga babban shafi
euro

Bankunan Turai sun bayyana damuwa game da tsuke bakin aljihu

Gamayyar kungiyoyi masu hada hadar kudi a Duniya sunce matakin tsuke bakin aljuhun gwamnatocin kasashen Turai, yana gurgunta habakar tattalin arzikin yankin inda bankunan suka nemi yin sassauci ga tsarin domin ci gaba da kashe kudade musamman kasar Jamus.

Charles Dallara, Shugaban gamayyar Bankun Turai
Charles Dallara, Shugaban gamayyar Bankun Turai REUTERS/Yiorgos Karahalis
Talla

Kasashe masu karfin bunkasar kasuwanci a Duniya, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen girgije yawan Bashin da kasar Girka ta yi fama da shi, sun fayyace karara, yadda tattalin arzikin kasashen yankin Euro yaci karo da mummunan Karo daya haifar da zazzabi mai tsanani ga harkokin kasuwancinsu, suna masu bayyana cewar matakin da aka dauka bai isa ba.

Shugaban gamayyar wadannan kasashen Cif Charls Dallara, yace fifikon da kasashen suka bayar ga shirin tsuke bakin aljihu ya yi dai dai idan aka gudanar da shirin bai daya.

Mista Dollara yace Makon da gwamnatocin yankin Euro ke yi ya taimaka ainun ga daidaita bukatunsu na cikin Gida gaba daya.

Asusun bada lamuni na Majalisar Dinki Duniya IMF ya bukaci kasashen ci gaba da aiwatar da shirin tsuke bakin Aljihu a kasashe kamar Girka da Spain wadanda matsalar tafi shafa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.