Iran ta dauki alhakin harba makamai masu linzami cikin Iraqi
Kasar Iran ta dauki alhakin harba makamai masu linzami kan birnin Irbil da ke arewacin kasar Iraqi, wadanda ta ce ta yi nufin su afkawa wata cibiyar kasar Isra’ila ne.
Wallafawa ranar:
Kafin sanarwar ta Iran dai, hukumar lardin Kurdistan da ke Iraqi ta ce makamai masu linzami 12 ne aka harba kan birnin na Irbil, wadanda suka jikkata fararen hula biyu da kuma rusa wasu gine-gine.
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun tabbatar da harba makaman, suna masu ikirarin kai hari kan wuraren da Isra'ila ke amfani da su.
An dai sha kai hari kan kadarorin Amurka da kuma dakarun hadin gwiwa da rokoki da kuma jirage marasa matuka a kasar Iraqi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu