Isa ga babban shafi

Saudiya da Qatar sun koka kan rashin kulawa da rikicin Gabas ta Tsakiya

Saudiya da Qatar sun bayyana bacin ransu kan rashin kulawa da rikicin Gabas ta Tsakiya da manyan kasashen duniya ke yi, a daidai lokacin da kasashen yammacin Turai ke matsa musu lamba kan su nuna goyon baya ga Ukraine da Rasha ta mamaye.

Ministan harkokin wajen kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al- Thani.
Ministan harkokin wajen kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al- Thani. REUTERS - Mohamed Azakir
Talla

Yayin da yake tsokaci kan lamarin, ministan harkokin wajen kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al- Thani ya ce tashin hankali da tagayyarar mutanen da ake gani a  a Ukraine, da kowa ke magana a kai, an dade ana ganin makamantansu dama wadanda suka zarce na. yanzu a kasance kasashe da dama na yankin Gabas ta Tsakiya tsawon shekaru, kuma babu abin da ya faru.

A cewar ministan na Qatar wanda yake Magana a wani taron tattaunawa a birnin Doha, manyan kasashen duniya bas u taba jajircewa wajen kawo karshen tashin hankalin da al'ummar Syria, ko na Falasdinawa da ‘yan Libya, da ‘yan Iraqi, ko kuma ‘yan Afganistan da ‘yan Yemen ke ciki ba, kamar yadda suka tashi tsaye kan halin da Ukraine ta shiga bayan mamaye ta da Rasha ta yi.

Saudiyya mai arzikin man fetur ko kuma Qatar mai arzikin iskar gas, dukkansu kawaye ne ga kasashen Yammacin Turai,  sai dai har yanzu basu bayyana wani matsayi kwakkwara ba wajen caccakar yakin da Rasha ke yi a Ukriane, saboda alakar kusancin da ke tsakaninsu.

Turai da Amurka na fatan kasashen biyu za su kara habaka samar da mai da iskar gas don taimakawa wajen rage dogaron da kasashen yammacin Turai ke yi kan kayayyakin Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.