Isa ga babban shafi
Zeben - Lebanon

Hezbollah ta 'Yan shi'a ta rasa rinjaye a Majalisar Dokokin Lebanon

Kungiyar Hezbollah ta ‘yan Shi’a da kawayenta a kasar Lebanon sun gaza samun rinjaye a majalisar dokokin kasar, kamar yadda sakamakon zaben majalisar da aka yi kwanaki 2 da suka wuce ya nuna ranar Talata, yayin da ‘yan takara masu zaman kansu suka ba da mamaki da nasarar da suka samu.

Magoya bayan kungiyar Hizbullah sun daga hotunan shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da tutocin kungiyarsu, a lokacin yakin neman zabe, a yankin kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon, Talata, 10 ga Mayu, 2022. Shekaru da dama na cin hanci da rashawa da rashin gudanar da mulki, lamarin da ke janyo rarrabuwar kawuna na makaman kungiyar Hizbullah ya kasance a tsakiyar zaben da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata kan sabuwar majalisar wakilai mai wakilai 128. (AP Photo/Hussein Malla)
Magoya bayan kungiyar Hizbullah sun daga hotunan shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da tutocin kungiyarsu, a lokacin yakin neman zabe, a yankin kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon, Talata, 10 ga Mayu, 2022. Shekaru da dama na cin hanci da rashawa da rashin gudanar da mulki, lamarin da ke janyo rarrabuwar kawuna na makaman kungiyar Hizbullah ya kasance a tsakiyar zaben da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata kan sabuwar majalisar wakilai mai wakilai 128. (AP Photo/Hussein Malla) AP - Hussein Malla
Talla

Cikakken sakamakon da ma’aikatar cikin gidan kasar ta sanar kwanaki 2 bayan zaben ya nuna cewa babu wata kungiya ko jam’iyya da za ta yi rinjaye a jam’iyyar mai kujeru 128, lamarin da masu sharhi kan al’amuran siyasa suka bayyana fargabar cewa ka iya janyo yanayi na tankiya da dambarwa.

Fashewar Beirut

Zaben, wanda shine na farko tun bayan da Lebanon ta dandana kudarta sakamakon matsalar tattalin arziki mafi radadi da ta taba fuskanta, da kuma mummunar fashewar da ta auku a tashar jiragen ruwan Beirut a shekarar 2020, na a matsayin sharadi na samun tallafi mai mahimmanci daga asusun bada lamuni na duniya.

A majalisar dokokin kasar da ta gabata, Kungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran da kawayenta na da kujeru 70, amma yanzu ta samu kasa da kujeru 65 da take bukata don ci gaba da kasancewa mai rinjaye.

Yanzu jam’iyya mafi karfi a cikin masu hamayya ita ce Christian Lebanese Forces na tsohon jagoran ‘yan tawaye, Samir Geagea, wadda ta lashe karin wasu kujeru a majalisar a wannan zabe da aka yi.

Zanga-zanga

Akalla ‘yan takara masu zaman kansu 13, wadanda suka goyi bayan zanga zangar shekara 2019 ne suka samu shiga majalisar dokokin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.