Isa ga babban shafi

Amurka ma ta sha tafka kuskure - Saudiyya

Mahukuntan Saudiyya sun ce sun kagara su manta da batun mutuwar dan jaridar nan Jamal Khashoggi, kwana guda bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya tada batun a ganwarsa da yeriman kasar mai jiran gado  Mohamed bin Salman. 

Yerima mai jiran gado na Saudiyya, Mohamed Ben Salman.
Yerima mai jiran gado na Saudiyya, Mohamed Ben Salman. AFP - HO
Talla

Tashar Al-Arabiyya ta kasar saudiyya ta ruwaito wani jami’in gwamnatin kasar na cewa kisan Khashoggi kuskure ne, kuma Amurka ma na tafka kuskure, inda ya yi nuni da yadda ta zargi Iraki da tara makaman kare dangi amma kuma sai aka sami akasin haka.

Tankiya tsakanin Biden da bin Salman ta ta’azzara gabanin haduwarsu, musamman ma tun lokacin da gwamnatin Biden ta fito da wani sakamakon binciken da ta gudanar, wanda ke zargin Mohamed bin Salman da bada umurnin kisan Khashoggi tare da yin gunduwa gunduwa da shi a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santanbul na Turkiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.