Isa ga babban shafi

Shirin gudanar da zanga-zangar adawa ya haifar da fargaba a Iraki

Jami'an tsaron Iraki sun kasance cikin shirin ko ta kwana a birnin Bagadaza a yau litinin, yayin da tashe-tashen hankula ke kara ta'azzara, bayan da magoya bayan Moqtada Sadr, da ke adawa da mabiya Shi’a, suka yi kira da a gudanar da zanga-zanga.

Magoya bayan fitaccen malamin kasar Sadr
Magoya bayan fitaccen malamin kasar Sadr AP - Hadi Mizban
Talla

Tun ranar Asabar, magoya bayan Sadr suka mamaye majalisar dokoki a yankin Green Zone duk da matakan tsaron da aka tsananta wanda kuma ke da gine-ginen gwamnati da ofisoshin MDD.

Sun fara zanga-zangar ne domin mayar da martani ga nadin da kawancen jam'iyyun adawa suka yi na matsayin kujerar fira minista.

Jami’an tsaro sun kafa shingaye akan hanya da wuraren binciken ababen hawa, gabanin kiraye-kirayen da masu goyon bayan tsarin hadin gwiwa da aka shirya za a fara da misalin karfe 5:00 na yamma agogon kasar (1400 agogon GMT).

Zanga-zangar "ba ta nuna adawa bace ga wata kungiya ba", in ji magoya bayan Sadr a shafukan sada zumunta.

Ana sa ran za a gudanar da zanga-zangar ne a kan hanyar da ta kai ga yankin Green Zone, wanda ba shi da nisa da inda dubban magoya bayan Sadr ke kwance a majalisar dokokin kasar, suna daga tutoci da hotunan Sadr.

Wani mai biyayya ga Sadr ya kuma yi kira ga magoya bayan malamin da su yi zanga-zanga a fadin lardunan Iraki, a zanga-zangar da za a yi lokaci guda.

A Iraki mai yawan kabilu daban-daban, kafa gwamnati ta kunshi tattaunawa mai sarkakiya tun bayan da Amurka ta mamaye kasar a shekara ta 2003 da ta hambarar da mulkin tsohon shugaba, Saddam Hussein, amma a cikin wannan yanayi na tsawon watanni 10 na rikicin siyasa ya bar kasar ba tare da gwamnati ba, ko sabon fira minista, ko kuma sabon shugaban kasa.

Gagarumin gangamin da Sadr ya yi da magoya bayansa a makonnin baya-bayan nan ya nuna irin tasirin siyasar da malamin ke da shi, wanda ya taba jagorantar mayakan sa-kai kan sojojin gwamnatin Amurka da na Iraki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.