Isa ga babban shafi
Iraki

Nakiyoyin da aka binne a karkashin kasa ya jikkata yara 500 a Iraki - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla yara sama da dari biyar ne suka mutu ko kuma suka jikkata sakamakon nakiyoyin da aka binne a kasar Iraki cikin shekaru biyar da suka gabata.

Babban magatakardar Majaalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Babban magatakardar Majaalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres AP - John Minchillo
Talla

Fiye da kashi 80 cikin 100 na yaran da abin ya shafa maza ne, in ji kungiyoyin kare hakkin yara na Majalisar Dinkin Duniya a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.

Sanarwar ta ce, duk da cewa Iraki ba ta fuskanci tashe-tashen hankula ba a cikin shekarun da suka gabata, abubuwan fashewar makamai da aka ajiye a wasu wuararen za su sake iya haifar da abubuwan da suka faru a shekarun baya.

Sanarwar ta kara da cewa, yara maza na fama da rashin daidaito sakamakon abubuwan da suka shafi bautarwa, kamar kiwo ko kuma aikin gwangwan domin dogaro da kai.

MDD ta ce ko da yake Iraki ta samu sassaucin tashe-tashen hankula a cikin shekarun da suka gabata, amma illar makaman fashewa ka iya sake yin kamari a shekaru masu zuwa.

Wani rahoto da kungiyar agaji ta Humanity & Inclusion ta fitar ya bayyana cewa, ana daukar kasar Iraki a matsayin daya daga cikin kasashen da aka fi samun gurbacewar ababen fashewa a duniya, inda fiye da murabba'in kilomita 3,200 na kasar ya gurbace da bama-bamai.

Wannan kayyyaki na ababen fashewa, bayanai  sun ce na kusa da kan iyakokin Iran, Kuwait da Saudi Arabiya, wadanda suka kasance yankunan da ke cikin rikici a cikin shekaru arba'in da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.