Isa ga babban shafi

Bincike ya nuna cewa ana da mayakan IS 400 zuwa 500 a Iraqi

Kungiyar IS na da mayaka tsakanin 400 zuwa 500 a Iraqi, wani babban jami'in sojan Irakin ne ya sanar da haka a yau lahadin, yayin da kungiyar masu da'awar jihadi ke ci gaba da kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula.

Mayakan ISIL suna azabtar da fararen hula
Mayakan ISIL suna azabtar da fararen hula © AP
Talla

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a cikin wani rahoto da aka buga a watan Fabrairu ya ambaci "mambobi da magoya bayan IS 5,000 zuwa 7,000" da aka tura tsakanin Iraki da Sirya, wadanda "kusan rabin" za su kasance masu fada da juna. Rahoton bai fayyace rabon su ba a kasashen biyu dake makwabtaka da juna.

Kama daga  shekarar 2014, kungiyar IS ta ga yadda ta ke kiran kanta "Khalifa" a karkashin tasirin hare-haren da aka kai a jere a wadannan kasashe biyu tare da goyon bayan kawancen kasashen duniya masu yaki da jihadi.

A karshen shekarar 2017 ne Iraki ta ayyana nasarar da sojojinta suka yi a kan mayakan jihadi, wadanda suka taba mamaye kusan kashi uku na kasar.

Wani yanki da ake gwabza fada tsakanin dakarun kasashen Duniya da mayakan jihadi a Iraqi
Wani yanki da ake gwabza fada tsakanin dakarun kasashen Duniya da mayakan jihadi a Iraqi © Creative Commons

 Janar Qaïs al-Mohamadawi, mataimakin kwamandan sashin ayyukan da ke sa ido kan hadin gwiwar jami'an tsaron Iraki ya ce "a cewar bayanai daga hukumomin leken asiri, jimillar mayakan IS ba su wuce 400 zuwa 500 ba , a larduna uku ko hudu."

"Kungiyar IS ta rasa yadda za ta iya jawo sabbin mayaka," in ji shi a wani taron manema labarai.

Bugu da kari, Janar din ya ambaci wani samame da aka kai a ranar 26 ga watan Fabrairu wanda ya ba da damar tarwatsa wani “sansanin horar da masu jihadi” a yammacin hamadar Iraki. Ya ce yayin shiga tsakani a lardin Al-Anbar, an kashe mayakan jihadi 22.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka buga a watan Fabrairu ga kwamitin sulhu ya tabbatar da cewa a Iraki, IS har yanzu tana aiki "a yankunan karkara masu tsaunuka, inda suke cin gajiyar bakin iyakar Iraki da Siriya tare da samun isasshen motsi don guje wa hare-hare. Sojojin Iraki".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.