Isa ga babban shafi

Sadr na Iraqi ya bukaci rushe Majalisar kasar nan da makwanni 2

Malamin Shi’ar Iraki mai dimbin magoya baya Moqtada Sadr, ya bukaci bangaren shari’a na kasar da ya rusa majalisar dokoki nan da makonni biyu masu zuwa don kawo karshen takaddamar da ake yi dangane da batun zaben sabon firaminista.

Jagoran mabiya shi'a na Iraqi, Moqtada Sadr.
Jagoran mabiya shi'a na Iraqi, Moqtada Sadr. © AFP
Talla

A sakon daya fitar jiya laraba, Moqtada Sadr ya bukaci magoya bayansa da su ci gaba da yin zaman dirshen a ciki da kuma zagayen ginin majalisar dokokin kasar har sai zuwa lokacin da suka cimma muradunsu.

Sadr ya ce akwai wadanda ke cewa wai sai majalisar kasar dokokin ta yi zama ne sannan za a rusa ta, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne, domin kuwa dokokin Iraki sun bai wa bangaren shari’a hurumin rusa majalisar idan aka shiga zaman tankiya.

Tun cikin watan oktoban da ya gabata ne aka gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a Iraki, to sai dai an gaza nada sabon firaminista saboda rashin fahinta tsakanin gungu biyu na ‘yan Shi’a da ke da sabani da juna, wato bangaren Sadr da kuma bangaren da tsohon firaminista Nuri al-Maliki ke mara wa baya.

Daukar dogon lokaci ba tare da zaben sabon firaministan ba, lamarin da ke kara jefa Iraki a cikin hali na rashin tabbas, yayin da ake fargabar yin fito-na-fito a tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.