Isa ga babban shafi

Magoya bayan Sadr dake zanga-zanga a Iraki sun mamaye Green Zone

Magoya bayan babban malamin kasar Iraki Moqtada Sadr sun kutsa harabar "Green Zone" mai cike da tsaro a Bagadaza inda suka mamaye majalisar dokokin kasar a wannan Asabar a wani rikicin siyasa da ke kara ruruwa.

Yadda magoya bayan malamin addinmin Iraki Muqtada al-Sadr suka taro a gadar dake zuwa Green Zone dake birnin Baghdad, 30/07/22.
Yadda magoya bayan malamin addinmin Iraki Muqtada al-Sadr suka taro a gadar dake zuwa Green Zone dake birnin Baghdad, 30/07/22. AP - Anmar Khalil
Talla

Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin kwanaki da magoya bayan Sadr ke shiga zauren majalisar, watanni bayan zaben da ya gaza kaiwa ga kafa gwamnati.

Masu zanga-zangar sun daga tutocin Iraki da hotunan malamin a cikin majalisar, kamar yadda wani mai daukar hoto na AFP ya ce.

Sun shiga ne bayan da dubban masu zanga-zangar suka yi dandazo a bakin wata gada da ta nufi yankin Green Zone kafin su jenye shingen da ke kare su, kamar yadda mai daukar hoton ya ruwaito.

Jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwa a kusa da wata kofar shiga yankin da ke da ofisoshin jakadancin kasashen waje da wasu gine-ginen gwamnati da kuma majalisar dokokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.