Sama da yara dubu 500 na fama da tsananin yunwa a Yemen - UNICEF
Asususn tallafa wa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF yace akalla yara dubu 540 ne ke fama da matsanaciyar yunwa a Yemen, da rashin abinci mai gina jiki, wanda kuma ke barzana ga lafiyar su.
Wallafawa ranar:
A cikin wani kundin bayani da asusun ya fitar, ya ce wannan matsala na kashe yaro guda cikin kowanne minti 10, a kasar da ke fama da tashin hankali.
Asusun na UNICEF ya kuma ci gaba da cewa bayan wadannan yara, akwai wasu guda miliyan 11 da ke neman tallafin gaggawa a kasar ta Yemen, inda kuma ake bukatar dala miliyan 488 a shekarar nan kadai don tallafa wa yaran.
Yakin da ake ci gaba da gwabzawa a kasar na ci gaba da taka rawa wajen jefa yaran cikin tashin hankali, tare da hana ma’aikatan jinkai shiga wasu yankunan don kai musu kayan tallafi, a cewar UNICEF.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu