Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashen Larabawa na taro a Saudiyya game da tsaron yankinsu

Shugabannin kasashen Larabawa da suka hada da shugaban kasar Syria Bashar Al Assad sun isa birnin Jeddah da ke gabar ruwan kasar Saudiyya domin gudanar da taron kungiyar kasashen Larabawa mafi muhimmanci a tarihinta.

Shugaban Masar Abdel Fattah El Sisi ne ya fara sauka a birnin na Jeddah daga cikin shugabannin da za su halarci taron.
Shugaban Masar Abdel Fattah El Sisi ne ya fara sauka a birnin na Jeddah daga cikin shugabannin da za su halarci taron. REUTERS - AHMED YOSRI
Talla

Bashar Al Assad, wanda aka mayar da kasarsa saniyar ware da kuma bayan shafe shekaru 12 ba ya halartar taron kungiyar, ya bar birnin Damascus da yammacin ranar Alhamis.

Ana sa ran shugaban na Syria zai yi jawabi a wajen taron da za a yi a Ritz Carlton da ke Jeddah.

Shugaban Masar Abdel Fattah El Sisi ne ya fara sauka a birnin na Jeddah daga cikin shugabannin da za su halarci taron.

Duk da sauye-sauyen manufofin ketare na baya-bayan nan a yankin, ko shakka babu taron na ranar Juma'a zai mayar da hankali ne kan makomar kasar Syria.

A ranar Larabar da ta gabata ne ministan harkokin wajen kasar Labanon Abdallah Bou Habib ya ce mayar da 'yan gudun hijirar Syria a Lebanon da yankin na daga cikin abubuwan da gwamnatin Lebanon ke ci gaba da aiwatarwa a kai, tare da hadin gwiwa da Syria.

Bou Habib ya musanta cewa ba za a samu komawar 'yan Syria da suka rasa matsugunansu daga Lebanon ba, wani muhimmin batu da zai tsaya tsayin daka a tattaunawa da gwamnatin Assad bayan komawarta cikin kasashen Larabawa.

Yunkurin da Saudiyya ta yi na mayar da kasar Siriya cikin kungiyar kasashen Larabawa, da dinke barakar da ke tsakanin ta da kasar Iran da kuma samar da zaman lafiya a kasar Yemen, duk wani yunkuri ne na kara tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.