Isa ga babban shafi

An kashe sojojin Isira'ila Uku a iyakar ta da Masar

Wani dan bindiga da ke sanye da kakin ‘yan sandan Egypt, ya harbe sojojin Isira’ila uku a wani hari da ya kai kan iyakon kasashen biyu.

Iyakar kasashen Isira'ila da Masar.
Iyakar kasashen Isira'ila da Masar. REUTERS/Nir Elias
Talla

Rundunar sojojin Isira’ila ta ce dan sandan Masarar ne ya kashe mata sojojin ta biyu a wani sansanin su da ke aikin samar da tsaron iyakar kasar da Masar, sannan kuma aka yi mutuwar kasko tsakanin wani sojan ta da jami’in dan sandan.

A nata tsokacin, rundunar sojojin Masar ta ce wani mai tsaron iyakar ta sun yi musayar wuta da sojojin Isira’ila a lokacin da ya ke kokarin dakatar da masu safarar miyagun kwayoyi.

Ministan tsaron Isira’ila Yoav Gallant ya ce ya gudanar da randadi da shugaban rundunar sojojin kasar a inda lamarin ya faru, kuma sojojin su za su gudanar da bincike a kai.

Egypt ce kasar Larabawa ta farko da ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isira’ila a shekarar 1979, ta re da kulla yarjejeniyar samar da tsaro a iyakokin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.