Isa ga babban shafi

Takaddama ta tsananta tsakanin Iran da Afghanistan kan kogin Helmand

Takaddama na kara tsananta tsakanin Iran da Afganistan kan hakkin mallakar kogin Helmand dake tsakaninsu, wanda ake ganin sauyin yanayi ne ke kara zurfafa rikicin.

Kogin Helmand ke tsakanin kasashen Iran da  Afghanistan
Kogin Helmand ke tsakanin kasashen Iran da Afghanistan AP - Heidi Vogt
Talla

Iran da Afganistan sun yi musayar wuta a ranar 27 ga watan Mayu a daidai lokacin da aka shiga wani yanayi na bukatar ruwan sha a yankin.

Kasashen dai sun shafe shekaru da dama suna takaddama kan mallakar kogin Helmand, wanda ‘yan kudancin Iran suka dogara da shi wajen gudanar da ayyukan noman rani. Yayin da gina madatsun ruwa da Afganistan ta yi a bangarenta ya kara tsananta lamarin a 'yan shekarun nan.

Taliban

Dakarun Taliban na Iran da na Afghanistan sun gwabza fada a kan iyakar kasar makonni biyu da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama, yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kan hakkin mallakar kogin a tsakanin Tehran da Kabul.

Kowannensu na zargin juna da soma harbi, Iran da Afganistan na kara daukar matsayar yaki a kan wannan kogi, saboda ruwan sha ganin yadda sauyin yanayi ke kara ta'azzara matsalar rashin ruwa a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.