Isa ga babban shafi

Falasdinawa fiye da miliyan 1 sun tsere daga gidajensu a Gaza

Falasdinawa sama da miliyan 1 sun tsere daga gidajensu cikin mawuyacin hali a Zirin Gaza, a yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta ta sama a matsayin ramuwa kan farmakin da mayakan Hamas suka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.

Falasdinawan da suka tsere daga arewacin Zirin Gaza bayan samun mafaka a gine-gine Majalisar Dinkin Duniya.
Falasdinawan da suka tsere daga arewacin Zirin Gaza bayan samun mafaka a gine-gine Majalisar Dinkin Duniya. REUTERS - MOHAMMED SALEM
Talla

A karshen makon da ya gabata Isra’ila ta bai wa Falasdinawa fiye da miliyan 1 umarnin ficewa daga arewacin Zirin Gaza zuwa kudancinsa, yayin da take shirin kaddamar da farmaki ta kasa domin murkushe kungiyar Hamas.

Ragowar baraguzan wani gini da jiragen Isra'ila suka ragargaza a Zirin Gaza.
Ragowar baraguzan wani gini da jiragen Isra'ila suka ragargaza a Zirin Gaza. REUTERS - MOHAMMED FAYQ ABU MOSTAFA

Hotunan bidiyon da ke yawo a shafukan Intanet sun nuna yadda dubban Falasdinawan ke samun mafaka a makarantu da sauran gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya da ke yankin, bayan da suka tattara abinda za su iya dauka daga cikin kayayyakinsu.

Har yanzu dai al’ummar yankin na Gaza ba su da isasshen ruwa da lantarki da kuma Intanet, sakamakon datse su da Isra’ila ta yi da zummar kuntata wa kungiyar Hamas, matakin da kasashe da dama da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yi Allah wadai da shi.

Ya zuwa yanzu mutane fiye da 2,670 suka rasa rayukansu a Gaza, sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai wa, yayin da a nata bangaren ta ce ta rasa mutane sama da 1,400, ciki har da sojojinta kusan 300, skamakon dubban makaman rokar da mayakan Hamas ke harbawa kan Isra'ilar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.