Isa ga babban shafi

Macron ya soki faifan bidiyo na mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a yau Talata ya yi Allah wadai da kungiyar Hamas da ta watsa wani faifan bidiyo na wata mata 'yar Faransa mai sheidar takardar Isra’ila  da kungiyar ta yi garkuwa da ita tare da neman a sake ta ba tare da wani sharadi ba.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron © Reuters
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya na mai cewa “abin kunya ne a yi garkuwa da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a kuma nuna su a wannan mummunar hanya.”

Shugaban kasar Faransa Macron na sane da faifan bidiyon wannan mata mai suna Mia Shem kuma ya yi kira da a gaggauta sakinta ba tare da wani sharadi ba. Faransa ta kara da cewa "tana aiki tare da kawayenta domin kubutar da Faransawan da kungiyar ta Hamas ta yi garkuwa da su".

Wasu Falasdinawa yayin zanga-zangar nuna adawar mamayan Isra'ila
Wasu Falasdinawa yayin zanga-zangar nuna adawar mamayan Isra'ila Mohammed Salem/Reuters

Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta tattauna a ranar Lahadin da ta gabata da iyalan mutanen da aka kashe ko aka yi garkuwa da su ciki har da na Shem.

Sojojin Isra'ila
Sojojin Isra'ila AP - Ariel Schalit

A yammacin jiya Litinin ne,kungiyar ta Hamas ta watsa wani faifan bidiyo a tashar ta Telegram na "daya daga cikin fursunonin Gaza", wanda ke nuna wata budurwa tana magana da Yahudanci,tana samun kulawa sosai tare da neman a sake ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.