Isa ga babban shafi
Malawi

Kotu ta daure masu auren luwadi na shekaru 14

Kotun kasar Malawi ta daure masu auren luwadi biyu, ko wanne na tsawon shekaru 14 a gidan fursuna. Ta same su da laifin saba zaman takewa cikin wannan mako, kuma yau Alhamis a ka yanke hukuncin.Ma’auratan na luwadi Steven Monjeza dan shekaru 26 da Tiwonge Chibalanga dan shekaru 20, an cafke su cikin watan Disamba lokacin da suke shirin aure na gargajiya.Alkalin kotun Nyakwawa Uisiwausiwa ya ce, ya dauki matakin daurin mafi tsauri, saboda sauran yaran kasar ta Malawi su kauce daga shiga cikin neman yin aure masu jinsi iri daya.Tuni kungiyarkare hakkin bil Adam ta duniya, Amnesty International ta bukaci sanin mutanen nan take ba tare da wata ka’ida ba.Wani dan raji kare hakkin bil Adam na kasar ya ce wannan sharia zata bakanta sunan kasar a idon duniya.

Steven Monjeza (left) and Tiwonge Chimbalanga have been convicted after symbolically wedding each other.
Steven Monjeza (left) and Tiwonge Chimbalanga have been convicted after symbolically wedding each other. Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.