Isa ga babban shafi

An tsare shugaban tashar jirgin kasar Girka sakamakon hatsarin da ya auku

Shugaban sashen kula da zirga-zirgar jiragen kasa a Girka, na fuskantar tuhuma a kasar, inda yanzzu haka yake tsare, bayan wani mummunan hatsarin jirgin da ya auku da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 57, daidai lokacin da firaministan kasar ya nemi afuwar jama’a kan faruwar ibtila’in.

Yadda dalibai suka gudanar da zzanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar Girka
Yadda dalibai suka gudanar da zzanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar Girka AP - Petros Giannakouris
Talla

Fusatattun mutane ne suka yi maci a kan tituna, game da tashin tashin hankalin da ya auku, inda ‘yan kasar ke zargin an yi watsi da tsaro da kuma lafiyar jiragen kasa, suna masu nuna alhini ga wadanda abin ya shafa.

Wata majiya ta shari'a ta shaida wa AFP cewa an tuhumi Vassilis Samaras, mai shekaru 59 bisa zarginsa da hannu wajen mutuwar dimbin mutane, kuma a karkashin dokar kasar Girka, laifin ya shafi hukuncin daurin shekaru 10 ko kuma na rai-da-rai.

Da sanyin safiyar Lahadi, gabanin taron tunawa da mutanen da abin ya shafa a Athens, Firaminista Kyriakos Mitsotakis ya rubuta sako ga al'ummar kasar mai cike da alhini da kuma neman afuwa, tare da tabbatar wa ‘yan kasar cewa nan ba da jimawa za a dauki matakan gaggawa ga harkokin sufurin jiragen kasa.

Haka kuma kasar Girka za ta nemi taimako da shawarwari daga Hukumar Tarayyar Turai da kuma samar da kudade don inganta da sabunta tsarin layin dogo na kasar.

Yayin da gwamnatin ke neman sake tsayawa takara a watan Afrilu, ana ganin matakin ya zama dole ga Mitsotakis ya nuna fushinsa saboda irin wannan bincike a Girka na iya daukar shekaru da yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.