Isa ga babban shafi

Turkiyya ta kalubalanci Girka bisa zargin keta sararin samaniyarta

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gargadi Girka cewa za ta dandana kudarta idan ta ci gaba da muzgunawa jiragen yakin Turkiyya a tekun Aegean tare da nuna alamun daukar matakin soji.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya AFP - ADEM ALTAN
Talla

Kasashen mambobin NATO guda biyu da ba sa ga maciji da juna, sun jima suna takaddama kan iyakokin ruwa da na sama wanda ya kai ga atisayen sojojin sama da ayyukan shiga tsakani galibi a kusa da tsibiran Girka da ke kusa da gabar tekun Turkiyya.

"Yak u mutanen Girka, ku dubi tarihi. Idan kun ci gaba, za ku dandana kudarku, ”in ji Erdogan a wani taron gangamin da aka yi a birnin Samsun na tekun Black Sea.

Kasashen Turkiyya da Girka a tarihi sun samu sabani a kan batutuwan da suka hada da tashin jiragen sama da kuma matsayin tsibiran Aegean zuwa kan iyakokin ruwa da albarkatun ruwa a tekun Bahar Rum, da kuma yankin Cyprus a shekara ta 1974.

A ‘yan watannin baya-bayan nan dai Turkiyya ta koka kan abin da ta kira ayyukan tunzura jama’a da Athens ta yi, tana mai cewa irin wannan yunkuri na kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya.

A wani lamari makamancin haka, Ankara ta ce a karshen makon da ya gabata Girka ta yi amfani da tsarin tsaron sama da Rasha ta kera wajen musgunawa jiragen yakin Turkiyya a wani aikin leken asiri abin da ta kira "matakin adawa".

A cikin jawabinsa, Erdogan ya zargi Girka da "kokarin yi wa Turkiyya barazana da jirgin ta samfurin S-300".

Girka dai ta yi watsi da zarge-zargen kuma galibi tana zargin Turkiyya da wuce gona da iri a tsibirin kasarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.