Isa ga babban shafi

Taho-mu-gama tsakanin jiragen kasa biyu ya kashe mutane 36 a Girka

Akalla mutane 36 suka mutu yayinda wasu 66 suka jikkata a wani hadarin jiragen kasa da ya faru a birnin Larissa na Girka da tsakad daren jiya talata, ko da ya ke da dama daga cikin fasinjojin sun samu tsira da rayukansu.

Hadarin jirgin kasa a Girka.
Hadarin jirgin kasa a Girka. REUTERS - ALEXANDROS AVRAMIDIS
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa jiragen biyu sun yi taho mu gama ne da tsakaddaren jiya talata yayinda suka ritsa da wata mota ta daban da ke kan hanya wadda ta kone kurmus dauke da fasinja.

Masu aikin ceto sun yi nasarar kaiwa yankin da hadarin ya faru sa’o’I kusan 5 bayan faruwarsa inda suka iya nasarar zakulo masu sauran lumfashi a ciki.

Tuni jami’an tsaro suka kame daraktan tashar jirgin kasan dattijo mai shekaru 59 wanda aka alakanta hadarin da kuskuren shi.

Bayanai sun ce ko wanne lokaci daga yanzu ne za a sanar da hukuncin da za ayiwa dattijon wanda ke kula da aikin bayar da hannu a tashar jiragen kasan wadda ke da alhakin kulawa da layukan dogon da hadarin ya faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.