Isa ga babban shafi

Mata masu juna biyu sama da 80,000 ke mutuwa duk shekara a Najeriya - UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bayyana cewa a kalla mata  82,000 ne ke mutuwa duk shekara a Najeriya, sakamakon matsalolin da suka shafi juna biyu ko kuma yayin haihuwa. 

Blandine Mekpo, wata unguwarzoma yayin yiwa mata masu juna biyu karin bayani kan cutar AIDS a garin Bohicon dake kudancin Jamhuriyar Benin.
Blandine Mekpo, wata unguwarzoma yayin yiwa mata masu juna biyu karin bayani kan cutar AIDS a garin Bohicon dake kudancin Jamhuriyar Benin. AFP/Getty Images - DELPHINE BOUSQUET
Talla

Wannan na zuwa ne, yayin da hukumomin lafiya na duniya ke ci gaba da jan hankalin kasashe, musamman masu tasowa muhimmancin inganta shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu.

Majalisar Duniya ta ce rayuwar mata masu juna biyu, ko kuma yayin haihuwa na cikin matukar hadarin gaske a nahiyar Afirka, don haka ana bukatar samar da wani shiri na musamman da zai magance wannan matsala.

A cewar UNICEF, mata 225 ne ke mutuwa a kowace rana a Najeriya, sakamakon mace-macen mata masu juna biyu ko kuma yayin haihuwa, inda suke neman hukumomi su dauki matakin gaggawa don dakile wannan matsala.

Masana kiwon lafiya na danganta mace-macen mata masu juna biyu ko kuma yayin haihuwa na da nasaba ne da sakaci zuwa duba lafiyarsu a lokacin da ya dace, yayin da wasu kuma ke fama da rashin cibiyoyin kula da lafiya a yankunan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.