Isa ga babban shafi
Bankin Duniya

Ngozi zata tsaya takarar shugabancin Bankin Duniya

Ministan kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala da Tsohon ministan kudin kasar Colombia Jose Antonio Ocampo tsakaninsu ne kasashe masu tasowa zasu gabatar a matsayin 'Yan takararsu a zaben sabon shugaban Babban Bankin Duniya a wani mataki na kalubalantar Amurka domin bayar da shugabancin babban bankin ga kasashe masu tasowa.

Ngozi Okonjo Iweala, Ministan kudin Najeriya a lokacin ta halarci wani Taron tattalin arzikin duniya
Ngozi Okonjo Iweala, Ministan kudin Najeriya a lokacin ta halarci wani Taron tattalin arzikin duniya REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Kamfanin Dillacin Labaran Reuters yace Okonjo-Iweala da Ocampo wadanda masana tattalin arziki ne sun samu goyon bayan kasashen Brazil da Afrika ta kudu domin kalubalantar Amurka.

Sai dai har yanzu Amurka na iya lashe kujerar shugabancin Bankin saboda goyon bayanta ga kasashen Yammaci inda ake hasashen wani Ba’amurke shi zai gaji Robert Zoellick wanda ya kudurta yin murabus a lokacin da wa’adin shugabancin shi zai kawo karshe a watan Yuni.

Ranar Juma’a ne ranar karshen gabatar da ‘Yan takara, kuma shugaban Amurka Barrack Obama yace Amurka zata gabatar da dan takara kafin lokacin.

Mambobin Kasashe 187 zasu zabi wanda zai gaji Robert Zoellick.

Kamfanin Dillacin Reuters ya ruwaito cewa kasar Brazil zata marawa Ocampo baya wanda Farfesa ne a Jami’ar Colombia a birnin New York.

A yau Laraba ne kuma ko ranar Juma’a ake hasashen za’a zabi Okonjo-Iweala cikin ‘Yan Takara.

Okonjo-Iweala tsohuwar Jami’a ce a babban Bankin duniya inda bayan zabensa Shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Jonathan ya nemi taimakonta domin karbar mukamin Minista don taimakawa ci gaban gwamnatinsa.

Ana hasashen Kasashe masu Tasowa zasu goyi bayan takarar Okonjo-Iweala da Ocampo da suka hada da kasashen China da India.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.