Isa ga babban shafi
Wasanni

Wasan Langa cikin wasannin gargajiya da aka gudanar a Lagos

Wallafawa ranar:

Shirin Duniyar Wasannin ya leka ne filin wasan Langa, Wasam gargajiya da ake gudanarwa a cikin jerin wasannin kasa a birnin Lagos shiyar kudu maso yammacin Najeriya inda Jahohin kasar 15 ne suka shiga wasan da suka hada da jahohin Arewa da kuma wasu daga yankin kudanci.

Wasan Langa da aka kara tsakanin Jahohin Najeriya a Birnin Lagos
Wasan Langa da aka kara tsakanin Jahohin Najeriya a Birnin Lagos RFI/Awwal Janyau
Talla

Wasan langa wasan gargajiya ne na Hausawa da aka dade ana yi, kuma wasa ne na matasa da suke yi a lokacin Kaka bayan an gama samun amfanin gona. Yawanci kuma matasa sukan gudanar da wasan da dare idan sun ci abinci bayan sallar Isha’i.

A gargajyance dai ana gudanar da wasan ne tsakanin mutane biyu ko fiye da haka ya dangata da adadin matasan da ke wasan. Kuma ‘yan wasan langa sukan lankwashe kwafarsu ne a bayansu, su rike babban yatsansu da hannu ko dai kafar hagu ko ta dama suna tafiya da kafa daya, daga nan sai su fara kai wa juna hari.

A tsarin wasan Langa da aka gudanar a Lagas ‘yan wasa 14 ne ke kara wa, kowane gida yan wasa bakwai ne kuma wasan kala uku ne “Ruwa” da “Kawo Shi” da “Ture shi”.

A cikin Shirin za ku ji yadda ake gudanar da Wasan da kuma fatar masu gudanar da don ganin wasan Langa ya shiga jerin wasannin da ake gudanarwa a wasanni Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.