Isa ga babban shafi
Wasanni

Matsalar Wariyar Launin Fata a Kwallon kafa

Wallafawa ranar:

Shirin Duniyar Wasannin ya diba matsalar wariyar launin fata ne da ake samu a kwallon kafa a kasashen Turai da ake dangantawa a matsayin annoba inda ‘yan wasa da masoyansu bakaken fata ke fuskantar walakanci da kaskanci. Al’amarin da har yanzu hukumar FIFA da ke kula da kwallon kafa a duniya bata shawo kai ba.

Alkalin wasa Mark Clattenburg da  John Mikel Obi ya zarga yan nuna masa wariyar Launin Fata
Alkalin wasa Mark Clattenburg da John Mikel Obi ya zarga yan nuna masa wariyar Launin Fata
Talla

Wannan batu na wariyar launin fata shi ne a kullum ke mamaye kafafen yada labaran duniya inda a makon jiya Peter Herbert, shugaban kungiyar lauyoyi bakaken fata ya yi Zargin Hukumar FA da ke kula da kwallon kafa a Ingila tana nuna wariya wajen rashin kin daukar matakan da suka dace don magance matsalar.

Wannan zargin kuma ya yi daidi ne da zargin da hukumar FA ta yi wa shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter a wata hira da ya yi da kafar yada labaran CNN a kwanakin baya inda hukumar FA da WAsu ‘Yan wasa suke ganin kalaman Shugaban sun sabawa Tunani.

Wannan kalaman na Blatter na zuwa ne bayan zargin dan wasan Liverpool Luiz Suarez da nuna wariya ga dan wasan Manchester United Patrice Evra dan kasar Faransa.

Kafin wannan ma akwai takaddama tsakanin jagoran ‘yan wasan Chelsea John Terry da Anton Fardinand da ke wasa a QPR kanin Rio Ferdinand.

Yanzu kuma rikicin ya dawo ne ga hukumar FA inda shugaban lauyoyi bakaken fata yace Hukumar tana daurewa matsalar gindi bayan ta ki gabatarwa 'yan sanda koken da dan wasan Chelsea, John Mikel Obi, ya yi a kan alkalin wasa Mark Clattenburg na nuna masa wariyar launin fata. A lokacin wasa tsakanin Chelsea da Manchester United.

Sai dai kuma shugaban FA, David Bernstein, ya yi watsi da zargin yana mai dangata bayyanan Herbert a matsayin basu da Tushe balle makama.

Shirin Duniyar Wasannin ya zanta da Tijjani Babangida Tsohon dan wasan Super Eagle na Najeriya da Dahiru Sadi game da wannan batu. Shirin Kuma yaji tabakin Masoya kwallon kafa domin jin Ra'ayinsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.