Isa ga babban shafi
Najeriya

Babban Kotu a Abuja ta bada Belin Shugaban Majalisar Dattijai da Mataimakin Sa

A Najeriya, Babbar Kotun Tarayyar dake Abuja, karkashin mai sharia Yusuf Halliru ta bayar da belin Shugaban majalisar Dattijan kasar Abubakar Bukola Saraki da Mataimakin sa Ike Ekweremadu da kuma tsohon Akawun Majalisar Dokokin kasar Salisu Maikasuwa da wani mataimakin sa.

Shugaban Majalisar Dattijai na Najeriya Abubakar Bukola Saraki na Rantsuwar Kama aiki ranar 9 ga Juni, 2015
Shugaban Majalisar Dattijai na Najeriya Abubakar Bukola Saraki na Rantsuwar Kama aiki ranar 9 ga Juni, 2015 REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A yau littini aka gurfanar dasu gaban kotun ana zargin su da aikata laifuka biyu da suka shafi sauya dokokin aikin majalisa ba tare da izini ba.

Saidu Mohammed Diri, Lauyan Gwamnati ya shaidawa manema labarai cewa yau dai sun gurfanar da mutanen hudu da ake tuhuma saboda sun hada kai sun kirkiro wata doka sun shigar da ita cikin dokokin majalisa.

Shima  Lauyan wadanda ake tuhuma Joseph Daudu ya bayyana cewa kowane bangare sun gabatar da jawabansu ga kotu.

Kotu dai ta bayar da belin su mutane biyu ciki ana bukatar mai gida a Garki, ko  Apo ko  Maitama.

Mai sharia ya tsaida ranar sha daya ga watan gobe domin ci gaba da sharia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.