Gwamnatin Najeriya za ta fara ciyar da dalibai
Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta fara aiwatar da shirinta na ciyar da daliban makarantun Firamare kimanin miliyan biyar da dubu 500 da ke fadin kasar nan da watan Satumba mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Shugabar shirin ta kasa ce, Abimbola Adesanmi ta sanar da haka a yayin taron masu ruwa da tsaki kan shirin ciyar da dalibai abinci kyauta a garin Abeokuta da ke jihar Ogun.
Mrs. Adesanmi ta ce, gwamnatin za ta fara bayar da abinicin ne ga daliban aji 1 zuwa 3 kafin daga bisani ta fara bai wa daliban azuzuwan gaba, idan tattalin arzikin kasar ya inganta.
A jihar Ogun kadai, akwai kimanin dalibai dubu 200 da ke matakin aji daya zuwa 3 a makarantun gwamnati dubu 1 da 154 kamar yadda gwamnan jihar Ibikulne Amosun ya bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu