Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai dau mataki kan kisan ‘yan Shi’a

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da kungiyoyin kare hakkin Bil Adama na duniya daukar matakan da suka dace dangane da rahotan binciken arangamar da akayi tsakanin sojojin Najeriya da magoya bayan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari Francois Picard/France 24
Talla

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta bayar mai dauke da sanya hannun Garba Shehu tace shugaban na nazari kan rahotan binciken da akayi, inda ya jaddada matsayin sa na kare hakkin Bil Adama.

Sanarwar tace gwamnatin Najeriya tana kan bakar ta na tababtar da bin doka da oda saboda haka duk wani martani da zata gabatar zai bi wannan mataki na dokar kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.