Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam'iyyar PDP ta dage babban taronta zuwa shekara guda

Taron Jam’iyyar PDP da aka gudanar a garin Fatakwal ya cinmma matsayar karawa kwamitin riko na shugabancin Jam’iyyar wa’adin shekara guda.

Filin taron Jam'iyyar PDP a Fatakwal da jami'an tsaro suka yi wa kawanya
Filin taron Jam'iyyar PDP a Fatakwal da jami'an tsaro suka yi wa kawanya
Talla

A baya wata babbar kotu a garin Abuja ta bada umurnin hani kan gudanar da babban taron jam’iyyar na zabar sabbin shuwagabanni, wanda hakan ya sa jami’an tsaro suka yi wa inda Jam’iyyar ta shirya gudanar da taron kawanya.

A zantawarsa da wakilin sashin Hausa na RFI Dr Ibrahim Umar mataimakin shugaban kwamitin tantance ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar ta PDP, ya ce wannan ta sa jiga- jigan jam’iyyar gudanar da taron a fadar gwamnatin jihar Rivers dake Fatakwal, inda suka yanke shawarar kara wa’adin rikon Jam’iyyar karkashin Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Sanata Ahmad Makarfi.

A baya bangaren tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff ya yi nasarar samun umurnin babbar kotu dake babban birnin tarayyar Najeriya Abuja Karkashin Justice Abang kan dakatar da duk wani taron Jam’iyyar ta PDP.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.