Jami'an tsaro sun janye daga kawanyar da suka yi wa Shi'a a Kaduna
Jami’an Soji da ‘Yan sanda a Najeriya sun janye daga kawanyar da suka yiwa mabiya Mazhabar Shi’a a Masallacin Markaz da ke titin Zango a Jihar Kaduna.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A jiya Talata ne dai jami’an tsaron suka yiwa mabiya Mazhabar Shi’a kawanya, yayin da suka taro domin gudanar da addu’o’i a Masallacin a ranar Ashura.
Wani shaidar gani da ido ya ce ba’a samu wani tashin hankali ba a wurin, kuma babu wanda aka kama, kasancewar kawo yanzu kowa ya watse daga wajen.
Tun da fari dai kimanin motocin jami’an tsaro 18 ne suka yiwa masallacin na Markaz kawanya kafin daga bisani wata kungiyar tabbatar da ‘yancin gudanar da ibada ta Addinin Musulunci da ke Birtaniya ta yi kira ga jami’an kan su janye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu