Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Shi'a sun mutu a wasu Jihohin Najeriya ranar Ashura

Rahotanni sun ce an yi arangama tsakanin jami’an tsaro da mabiya mazhabar Shi’a a sassa da dama na Najeriya a daidai lokacin da ‘yan Shi’ar ke juyayin zagayowar ranar Ashura.

Ranar Ashura ba ta zo wa 'yan shi'a da dadi ba a Najeriya
Ranar Ashura ba ta zo wa 'yan shi'a da dadi ba a Najeriya
Talla

A Funtua da ke jihar Katsina an kashe ‘yan Shi’a akalla 3 da dan sanda guda, yayin da a biranen Kano da Jos da Sokoto da kuma Kaduna, wasu da aka ce fararen hula ne suka afkawa ‘yan Shi’ar tare da kona wurarensu na ibada da asaran rayuka.

Sai dai wasu rahotanni da ba a tabbatar ba, sun ce ‘yan shi’ar 9 aka kashe a Katsina.

Da fari dai gwamnatin Jihohin da suka hada da Kaduna da Kano da Katsina da Kebbi sun haramtawa 'yan shi'a yin tattaki a wannan shekarar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.