Isa ga babban shafi
Najeriya

Tsagerun Niger-Delta Dake Njeriya Sun Ce Jibge Sojoji a Yankinsu Ya Sa Suke Sake Fasa bututun Mai

'Yan Tsagerun yankin Niger-Delta a Najeriya, sun bayyana cewa mamaye yankin su da sojan kasar suka yi na barazana ga tattaunawan sulhu, kuma shine ummal-habaisin sake kai munanan hare-haren kan bututun mai da fasa bututun dake yankunan su.

Shugaba Buhari jim kadan bayan  ya gana da Shugabannin yankin Neja Delta
Shugaba Buhari jim kadan bayan ya gana da Shugabannin yankin Neja Delta REUTERS
Talla

Tsagerun na Niger Delta Avengers, NDA sun fadi a shafin su ta yanar gizo cewa kada a zarge su da wani laifi saboda fasa bututun danyen mai dake yankin nasu ganin yadda Gwamnati ke kara jibge masu sojoji dake barazana ga mazauna yankin.

Kalaman ‘yan tsageran na zuwa ne kwanaki kadan bayan da suka kai wani kazamin hari inda suka Burma bututun danyen mai na Trans Forcados Pipeline.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.