Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bayanai kan rusau a Legas

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci samun bayani daga gwamnatin Najeriya da kuma ta Jihar Legas da ke kasar, game da rushe dubban gidaje da aka yi na unguwannin Otodo Gbame da ke bakin ruwa birnin na Legas, duk da cewa wata babbar kotu a jihar ta yanke hukuncin dakatar da matakin.

Unguwar Makoko da ke bakin ruwa a jihar Legas, daya daga cikin wurare da gwamnati ta bada umarnin rushe daruruwan gidaje.
Unguwar Makoko da ke bakin ruwa a jihar Legas, daya daga cikin wurare da gwamnati ta bada umarnin rushe daruruwan gidaje.
Talla

Kungiyoyin fararen hula sun ce sama da mutane 30,000 suka rasa muhallansu sakamakon matakin na rusau da gwamnati ta dauka.

Babbar jami’ar da ke wakiltar Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya wajen tattara rahotanni kan samar da muhalli ga jama’a, Leilani Farha, wadda ta jaddada cewa samar da muhalli ga al’umma hakki ne da ya zama tilas kan gwamnati ta sauke shi, ta ce dole gwamnatin Najeriya hadi da ta Legas su gabatar da gamsasshen bayani ga majalisar kan matakin da suka dauka.

Rahotanni sun ce akalla mutane 7 suka rasa rayukansu, sakamakon harbi cikin iska da suka yi yayinda suka kutsa cikin unguwannin da ke gabar ruwan na Legas.

Sai dai kuma rundunar ‘yan sandan jihar ta ce jami’anta sun yi harbin ne, domin kwantar da tarzomar da ta tasamma barkewa tsakanin mazauna unguwannin.

A martaninsu mazauna Otodo Gbame sun musanta ikirarin rundunar 'yan sandan, inda suka ce makarkashiya ce kawai daga jami’an domin raba su da muhallansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.