Isa ga babban shafi
Najeriya

An Zarcewa Arewa Maso Gabashin Najeriya Da Shekaru 500 ta Fannin Ilmi- Inji Farfesa Njodi

Shugaban Jami'ar Maiduguri dake Arewaci Najeriya Farfesa Abubakar Njodi ya ce rikicin kungiyar Boko Haram ya maida yankin na Arewa maso gabashin Najeriya baya ta fannin ilmi da  shekaru 500.

Hoton jagoran Boko Haram da ke yaki da masu neman ilmi.
Hoton jagoran Boko Haram da ke yaki da masu neman ilmi. HO / BOKO HARAM AFP / AFP
Talla

Farfesa  Njodi ya yi nuni da cewa tun kafin  bullar kungiyar Boko Haram akwai masana dake ganin an bar yankin a baya da kamar shekaru 150 ta fannin ilmi bisa sauran sassan kasar musamman kudanci, sai gashi kuma an sami wannan bala'i.

Ya shaidawa tawagar komitin Asusun tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya cutar da suka ziyarce shi a Maiduguri, don jajanta masa sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai jami'ar da yayi sanadiyyar mutuwar ma'aikata uku, cewa ta fannin ilmi dai yankin na bukatar jama'a su mike sosai a tallafa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.