Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a dawo da ‘yan gudun hijrar Najeriya 78,000 gida

Gwamnatin jahar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta shirya don ta kwaso ‘yan gudun hijrar kasar kimanin dubu saba’in da takwas gida daga kasar Kamaru.

'Yan gudun hijra Najeriya sama da 78,000 ne ke zaune a sansaninsu dake a kasar Kamaru
'Yan gudun hijra Najeriya sama da 78,000 ne ke zaune a sansaninsu dake a kasar Kamaru REUTERS/stringer
Talla

Dubban ‘yan gudun hijrar na daga cikin wadanda tsananin rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa gidajensu inda suka nemi mafaka a makwabciyar kasar.

A makon da ya gabata ma dai ‘yan gudun hijrar sun yi barazana takawa da kafarsu daga Kamaru zuwa Najeriya muddun gwamnati ta ki mutunta bukatarsu ta mayar dasu garuruwansu.

Rikicin Boko Haram ya tilastawa mutane fiye da miliyan daya da rabi rasa matsuguni baya ga wasu sama da dubu uku da suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankula na fiye da shekaru hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.