Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Boko Haram ta sako sama da mutane dubu 12

Ministar tsaro a Najeriya, Mansur Ali, ya ce zuwa yanzu kungiyar Boko Haram ta saki mutane dubu 12 wadanda ta yi garkuwa da su a kasar a shekarun baya.

'Yan matan sakandaren Chibok 82 da mayakan Boko Haram suka sako a baya bayannan.
'Yan matan sakandaren Chibok 82 da mayakan Boko Haram suka sako a baya bayannan. twitter
Talla

Ministan ya ce cikin mutanen da mayakan suka sako akwai ‘yan mata chibok sama da 100 da gwamnatin Buhari ta ceto a rukunni biyu, bayan tattaunawar da ta yi da kungiyar, da tallafin masu shiga tsakani kamar yadda kamfanin dilancin labaran kasar NAN ya rawaito.

Tun bayan kaddamar da tada kayar baya da kungiyar Boko Haram ta yi shekarar 2009, mayakanta sun yi sanadin rasa rayukan mutane dubu 100 da yin garkuwa da dudbai a yankunan da ke arewacin Najeriya, musamman arewa maso gabashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.