Isa ga babban shafi
Najeriya

Sabon Bidiyo Boko Haram ,farfaganda ce- Kuka Sheka

Kakakin rundunar sojin Najeriya Brigadiya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya bayyana sabon bidiyon da mayakan kungiyar Boko Haram suka fitar a matsayin Damisar takarda, tare da bukatar jama’a su yi watsi da barazanar da mayakan suka yi.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram sanye da kayan soja
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram sanye da kayan soja REUTERS/Zanah Mustapha
Talla

Cikin Bidiyon dai mayakan sun yi barazanar kai hare hare a birnin Abuja, tare da nuna wasu daga cikin ‘yan matan sakandaren Chibok 3 da har yazu ke hannunsu dauke da bindigogin AK 47, inda suma ke barazanar kai hare haren.
A cewar Birgediya Janar Kuka Sheka, mayakan sun rasa tudun dafawa ne, shi ya sa suke yin abinda ya kira da shure shure, wanda ya ce baya hana mutuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.