Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta fitar da sabon Bidiyo

Wani mutun da yace dan kungiyar Boko Haram ne a Nigeria ya fita da wani hoton bidiyo inda yake ikirarin cewa suna shirye-shiryen kaddamar da harin bama-bamai a birnin Tarayya Abuja.Wannan barazana na zuwa ne jim kadan bayan wani harin kunar bakin wake da wasu 'yan mata biyu suka kai Jami'ar Maiduguri inda nan take suka mutu.

'Yan matan Chibok 82 da aka kubutar tare da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
'Yan matan Chibok 82 da aka kubutar tare da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari rfi
Talla

Kamfanin Dillancin labaran Reuters ya sanar da cewa ya ga bayanan dake kunshe cikin wannan bidiyo.

Kamfanin  labarai na Reuters ya ce bai tantance sahihancin wannan hoton bidiyo ba.

Koda a kwanan baya Hukumar ‘yan sandan farin kaya ta DSS ta sanar da cewa ta gano wani shiri na kungiyar Boko Haram na kai hare-hare ofisoshin jakadancin Birtaniya da na Amurka a Nigeria.

A wani hoton bidiyo da Reuter ya gani, har da wata mace da akace tana cikin ‘yan matan Chibok da ba ta son barin kungiyar ta Boko Haram kuma an nuna ta  sabe da bindiga tana fadin cewa ba'a yi mata auren dole ba, kuma ba zata koma wajen iyayenta ba saboda basa bin Allah.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.