Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta biya masu fallasa kudin sata Naira miliyan 375

Gwamnatin Najeriya ta ware Naira miliyan 375.8 don biyan masu fallasa kudaden sata 20 da suka taimaka hukumomin kasar wajan gano Naira Biliyan 11.6.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa a kasar
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawa a kasar REUTERS
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Kudin kasar da ta tabbatar da sakin kudaden ta ce, a karon farko kenan da ake biyan mutane karkashin tsarin fallasa kudaden satar.

Sai dai gwamnati ba ta bada bayani ba game da mutanen da suka amfana da kudaden saboda dalilai na tsaro.

Ma’aikatar Kudin ta ce, matakin biyan ya nuna irin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta mayar da hankali don cika alkawarinta ga masu fallasar, wadda ke da muhimmanci wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Gwamnati na bai wa masu fallasar akalla kashi 5 cikin 100 na kudaden da suka bayar da bayanansu kuma aka gano su, amma an tanadi hukuncin dauri a gidan yari kan duk wanda ya fallasa bayanan karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.