Najeriya ta yi asaran Dala Triliyan 1 kan kin biyan haraji
Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi asarar kudin da ya kai Dala Triliyan guda a shekarar 2016 saboda yadda manyan kamfanonin kasashen waje da ke aiki a kasar suka ki biyan harajin da ya wajaba a kan su.
Wallafawa ranar:
Mukaddashin shugaban Najeriya Ferfessa Yemi Osibanjo ya bayyana haka, inda ya ke cewar wannan ya sa gwamnatin ta shiga wasu yarjeniyoyi da kasashen duniya domin hana yadda kamfanonin ke kwashe kudaden zuwa kasashen duniya da zummar kaucewa biyan haraji.
Osibanjo ya ce gwamnati na daukan matakan da suka dace wajen ganin irin wadanan kamfanoni sun sauke nauyin da ke kan su wajen biyan harajin da ya wajaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu