Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Jihohi 23 basu biya albashin watanni ba

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi a Najeriya, ta bukaci gwamnatin tarayya ta tsoma baki domin biyan ‘ya’yanta albashin da ya kama daga wata daya zuwa watanni 16 a wasu kananan hukumomi da ke jihohi 23 na kasar.

Wasu daga cikin ma'aikatan kananan hukumomi a kudancin Najeriya (jihar Osun) da ke neman a biyasu hakkokinsu na albashi.
Wasu daga cikin ma'aikatan kananan hukumomi a kudancin Najeriya (jihar Osun) da ke neman a biyasu hakkokinsu na albashi. herald.ng
Talla

Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Ibrahim Khaleel, ya ce matsalar ta fi tsananta ne a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Delta da suka gaza biyan albashin watanni 10 zuwa 16.

Sauran jihohin da matsalar rashin biyan albashin ta shafi ma’aikatan kananan hukumomin, sun hada da Kaduna, Oyo, da kuma Edo, da lamarin ya kama daga watanni 3 zuwa 10, yayin da jihohi irinsu Zamfara suka ki fara aiki da sabon tsarin biyan albashi mafi kankanta.

Jihohin Adamawa, Filato, Akwa Ibom, Rivers da kuma Ebonyi kuwa, sun gaza biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomin na watani hudu, ne yayinda kuma ma’aikatan ke bin jihar Tarab da kuma babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, albashin watanni uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.