Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan bindiga sun hallaka mutum 21 a kudancin Najeriya

Rahotanni daga jihar Rivers da ke kudancin Nigeria sun ce wasu ‘yan bindiga da aka gaza sanin manufarsu sun kashe Mutum 21 da ke hanyar komawa gida kafin wayewar garin jiya littini bayan sun kwana suna addu'o'i a Coci.

'Yan tawayen yankin Neja Delta a Najeriya
'Yan tawayen yankin Neja Delta a Najeriya (Photo : AFP)
Talla

Rahotanni na danganta lamarin da rikici tsakanin wasu kungiyoyin matsafa da basa ga maciji da juna, yayin da wasu majiyoyin ke danganta harin da sakaci ‘yan siyasan yankin.

Jami’an ‘yan sanda Jihar sun gaza tabbatar da adadin wadanda aka hallaka sai dai sun ce an kashe tare da jikkata wasu a karamar hukumar Onelga.

Daraktar Janar na hukumar kula da zirga-zirgan jiragen ruwa na kasa, Dakuku Peterside, wanda ya fito daga Jihar ya ce mutum 21 aka kashe a harin.

Jihar Rivers na daya daga cikin yakunan Neja Delta da ake fama da kungiyoyin 'yan tawaye masu tada zaune tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.