Isa ga babban shafi
Najeriya

An sako Turawan nan 5 da aka yi garkuwa da su a Najeriya

‘Yan tawayen Niger Delta sun saki wasu ‘yan kasashen waje guda 5 da suke garkuwa da su a gabar tekun Najeriya.

Tsagerun Niger Delta da suka shahara wajen yin garkuwa da Mutane
Tsagerun Niger Delta da suka shahara wajen yin garkuwa da Mutane AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

An sace turawan ne tun a watan Janairu da ya gabata, mutanen 5 sun kunshi ‘Yan kasar Philiphhines da Rasha da kuma Goergia.

Tuni ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Rasha ta tabbatar da sakin turawan inda tace ce suna kan hanyarsu ta dawowa gida

Ana dai ci gaba da fuskantar matsalar yawaitar  garkuwa da mutane a Najeriya musanman ma turawa dake a  yankin na Niger Delta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.