Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari na ganawa da Benue kan rikicin makiyaya

A wannan Litinin ake saran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi wata ganawa da shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya na jihar Benue a fadarsa da ke birnin Abuja don tattaunawa kan matsalar tsaron jihar da ta kai ga asarar rayukan dimbin jama’a.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa da rikicin makiyaya da manoma
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa da rikicin makiyaya da manoma REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugaba Buhari ya nuna damuwa matuka kan kisan mutanen, yayin da ake zargin Fulani makiyaya da aikata kisan duk da cewa, kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta sha musanta irin wannan zargi.

Wata majiya a fadar shugaba Buahari ta bayyana cewa, ganawar ta yau ta zama wajiba saboda yadda rikicin ya tsananta da kuma yadda ake ci gaba da cece-kuce akansa a sassan kasar.

Majiyar ta kara da cewa, ganawar za ta kuma mayar da hankali kan zargin da ake yi wasu gwamnatocin jihohin Najeriya na bada horo da makamai ga wasu kungiyoyi 'yan tawaye.

Wannan na zuwa ne bayan sojojin kasar sun ce sun cafke wasu mutane da suka amsa cewa, gwamnatin jihar Benue ta dauke su aiki tare da ba su horon sarrafa bindiga da kuma biyan su albashi a duk karshen wata, zargin da gwamnatin ta musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.