Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana zaman dar-dar a Jihar Benue

Rahotanni daga Makurdi a jihar Benue da ke tarayyar Najeriya sun ce, ana zaman dar-dar musamman a tsakanin Hausawa mazauna Birnin.Dama dai Jihar Benue na daga cikin yankunan kasar da a baya-bayan nan ake fuskantar tashe-tashen hankulan, lamarin da ke barazana ga tsaron kasar.

Tuni dai aka Jibge tarin Jami'an tsaro a Jihar ta Benue don tabbatar da tsaro tare da kawo karshen rikicin na Makiyaya da manoma.
Tuni dai aka Jibge tarin Jami'an tsaro a Jihar ta Benue don tabbatar da tsaro tare da kawo karshen rikicin na Makiyaya da manoma. AFP
Talla

Yanayin zaman zullumin, na zuwa kwanaki kadan bayan kisan gillar da aka yi wa mutane da dama a wasu kananan hukumomin jihar, da ake zargin wasu makiyaya ne suka aikata.

Alhaji Dan Bala Garba, wani mazaunin birnin na Makurdi, ya ce a halin yanzu sun kauracewa zirga-zirga saboda tsoron abinda zai biyo baya, ganin yadda tuni wasu daga cikin kabilun yankin suka fara kai harin daukar fansa kansu.

Ko a makon da ya gabata ma, sai da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya umarci babban sufeton 'yansanda Ibrahim Idris ya koma jihar ta Benue da zama don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

Haka zalika a dai cikin makon da ya gabata gwamnatin Jihar ta gudanar da jana'izar bai daya ga fiye da mutane 80 da suka mutu sanadiyyar rikicin Manoma da Makiyaya.

Duk da cewa Gwamnatin jihar ta zargi Fulani Makiyaya da aiwatar da kashe-kashen ta bakin mai bata Shawara kan harkokin tsaro Ali Tishahu, amma shugaban hadakar kungiyar Fulani na kasar Miyetti Allah ta bakin Alhaji Abdullahi Lalega ya musanta zargin yana mai cewa yanzu haka babu Fulani a Jihar ta Benue domin kuwa tuni Gwamnatin ta Kore su.

A bangare guda kuma Kungiyar ta Miyetti Allah ta zargi Gwamnatin Jihar da horar da wasu matasa don su rika kai hare-hare yayinda ta ke biyansu dubu goma sha biyar kowanne wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.