Isa ga babban shafi
Najeriya

Fadar Buhari ta mayar da martani ga CAN kan rikicin Fulani

Fadar gwamnatin Najeriya ta mayar wa kungiyar Kiristoci ta kasar, CAN martini wadda ta zargi shugaba Muhammadu Buhari da nuna kabilanci wajen tinkarar rikicin Fulani makiyaya a sassan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan rikicin jihar Benue da ya haddasa asarar rayukan jama'a da dama
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan rikicin jihar Benue da ya haddasa asarar rayukan jama'a da dama REUTERS
Talla

Mai magana da yawun kungiyar, Musa Asake ya shaida wa manema labarai cewa, zargin da ake yi wa Buhari na kokarin musuluntar da Najeriya a fakaice na dada tabbata musammam idan aka yi la’akari da abin da ya faru na kisan jama’a a jihar Benue.

A cewar Asake, Fulani makiyaya na samun kariya a karkashin mulkin Buhari ta yadda suke daukan Najeriya tamkar wani yanki da suka mamaye.

Asake ya ce, a maimakon cafke Fulanin da kuma gurfanar da su, jami’an tsaron Najeriya na ba su kariya duk da aikinsu na ta’addanci.

Sai dai a yayin mayar da martanin, mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam garba Shehu ya ce, abin takaici ne yadda Asake ya gaza bada kwakkwarar hujjar da ke nuna cewa Buhari ya karya dokokin Najeriya.

Shehu ya kara da cewa, shugaba Buhari ba ya barazana ga demokradiya da kundin tsarin mulkin kasar.

A cewar Shehu, ya kamata Asake ya tsame kansa daga harkokin siyasa a matsayinsa na jagoran addini

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.