Isa ga babban shafi
Najeriya

Matasan Ohanaeze sun bukaci makiyaya su fice daga yankunansu

Kungiyar matasan kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo OYC, ta umarci baki dayan Fulani makiyaya da su fice daga yankunansu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Matasan kungiyar Ohanaeze sun gargadi Fulani makiyaya da su fice daga yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Matasan kungiyar Ohanaeze sun gargadi Fulani makiyaya da su fice daga yankin kudu maso gabashin Najeriya. REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Sanarwar da shugabancin kungiyar Ohaneaze, OYC ya sanya wa hannu, ta ce ta dauki matakin ne sakamakon kisan gillar da ake yi wa daruruwan mutane a sassan Najeriya, wadanda kuma ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa.

Matasan na Ohaneaze sun bukaci gwamnatin Najeriya ta haramta ayyukan 'ya'yan kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah, ta kuma bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.

Matasan na Kabilar Ibo, sun gargadi makiyayan da su gujewa kin bin umarnin da suka basu na ficewa daga yankin.

An dai dauki tsawon lokaci ana zargin Fulani makiyaya da haddasa hasarar rayukan a sassan Najeriya, sakamakon rikice-rikicen da ake samu tsakaninsu da manoma musamman a arewacin Najeriya.

Sai dai a nata bangaren kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah ta bayyana cewa a mafi akasarin lokuta makiyayan ake tsangwama tare da zaluntarsu, kamar yadda ta bayanna a rahoton da ta fitar a cikin wannan wata na Janairu.

Rahoton kungiyar ya bayyana cewa akalla manbobinta makiyaya dubu daya aka hallaka, sakamakon rikice-rikicen da suke fuskanta tsakaninsu da manoma a sassan Najeriya.

Kungiyar ta kara da cewa baya ga mambobinta dubu guda da aka kashe, an hallaka musu shanu fiye da milyan biyu yayin rikicin da ya faru a jihohin Benue da Taraba dama wasu sassan kasar.

Sanarwar dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar na kasa Baba Othman-Ngelzarma ta kuma kalubalanci sahihancin ikirarin da gwamnatin Benue ta yi, na cewa Fulanin ne suka hallaka fiye da mutane 80 da ta yi wa jana’izar bai daya cikin makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.